✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya na kan gaba wajen noma da shan Tabar Wiwi a duniya — NDLEA

Sai dai ya ce za a iya shawo kan matsalar

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya wajen noma da shan Tabar Wiwi.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin bude wani taro kan kiyaye ta’ammali ga miyagun kwayoyi da hukumar ta shirya wa matan Gwamnoni a Abuja.

Ya ce matsalar shan kwaya na daya daga cikin manyan matsalolin da suke addabar duniya a halin yanzu.

A cewarsa, “Kadan daga cikin illolin shan kwaya shi ne kamuwa da cututtuka iri-iri da kuma mutuwa tun da kuruciya, kuma abubuwa ne da bai kamata da duk gwamnatin da ta san me take yi ba za ta zura ido a kai ba.

“Abin takaici Najeriya ma ta tsira daga irin wadannan matsalolin ba. A yanzu haka, kasarmu na da wasu alkaluma masu matukar tayar da hankali.

“Shekara hudu da suka shude, muna da mutum miliyan 10.6 da ke shan Tabar Wiwi, wanda hakan ke nuni da cewa muna cikin kasashen da ke kan gaba a wannan fagen a duniya,” inji shi.

Buba Marwa ya kuma ce Najeriya ta kuma zam tamkar kwadon shara ga miyagun kwayoyi da magunguna irin su Tramadol da Kodin, sannan ta zama cibiyar hada-hadar Hodar Iblis da Tabar Wiwi zuwa wasu kasashen.

Sai dai ya ce za a iya shawo kan matsalar idan aka rungumi kyakkyawa kuma nagartaccen tsarin magance matsalar, kamar irin wannan taron bitar.