✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da Saudiyya sun kulla yarjejeniyar yakar safarar migayun kwayoyi

Kasashen biyu sun amince don yin aiki tare wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da Babban Daraktar Hukumar Kula da Miyagun Kwayoyi na kasar Saudiyya (GDNC), sun kulla yarjejeniya kan yaki da safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasashen biyu.

Wannan shi ne batun da shugaban NDLEA Birgediya-Janar Buba Marwa da wakilin GDNC Kanal Naser Otaibi suka tattauna a ranar Litinin.

  1. Arsenal ta sayi Martin Ødegaard daga Real Madrid
  2. A kashe mutum, an kona gidaje 22 a Zangon Kataf

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Mista Femi Babafemi ya fitar ranar Laraba a Abuja, Marwa ya yi godiya ga tallafin da hukumomin Saudiyya ke bai wa Najeriya.

Marwa ya ce, “Bisa la’akari da bukatar hadin gwiwa mai dorewa, an cimma yarjejeniya tsakanin hukumomin biyu.”

Ya ce yarjejeniyar na da mahimmanci wajen yakar fataucin miyagun kwayoyi da abubuwan da ke haifar da tabin hankali.

“Wannan ya zama tamkar yarjejeniyar kwanan nan da muka kulla da kasar Gambiya,” in ji shi.

Marwa ya ce Najeriya ta dauki matakin yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma yin fataucinsu bisa ga goyon bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumar kan duk bukatunta don aiwatar da ayyukanta.

Shugaban na NDLEA ya roki gwamnatin Saudiyya da ta tallafa masa, musamman a fannin fasaha da bayar da gudummawar kayan aiki kamar na’urar bincike, dakin gwaje-gwaje da cibiyoyin gyara.

Ya kuma karbi goron gayyatar ziyarar Saudiya tare da fatan hakan zai ba da damar sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tsakanin hukumomin yaki da fataucin miyagun kwayoyi a kasashen biyu.

A nasa jawabin, wakilin GDNC, Otaibi ya ce wannan yarjejeniya za ta karfafa wa fannoni daban-daban domin shawo kan matsalar fataucin miyagun da NDLEA da GDNC suka sanya a gaba.