✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da Ghana sun cimma yarjejeniya kan iskar Gas

A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin Mai Fetur na kasa wato (NNPC) ya bayyana cewa ya warware takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnatin…

A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin Mai Fetur na kasa wato (NNPC) ya bayyana cewa ya warware takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnatin kasar Ghana kan batun bashin kudin iskar gas.

Najeriya na bin kasar Dala miliyan 170 na kudin iskar gas, abin da ya sa kasar nan ta yi barazanar rage yawan gas din da take tura wa Ghana idan ba ta biya bashin da ake bin ta ba.
Sanarwar NNPC, ta ce a yanzu an kulla yarjejeniya kan yadda Ghana za ta biya bashin ba tare da bata lokaci ba.
An cimma yarjejeniyar ce a ranar Litinin, bayyan wata tattaunawa tsakanin Shugaban Ghana John Dramani Mahama da shugaban NNPC, Ibe Kachukwu da kuma ministan makamashin Ghana, Kwabena Donkor.
kasar nan ce ke samar wa Ghana wani kaso na iskar gas da kasar ke bukata domin bunkasa samar da lantarki a Ghana.
A ‘yan kwanakin nan, Ghana na fama da matsalar karancin wutar lantarki abin da ya sa gwamnatin kasar ke fuskantar caccaka, musamman kasancewa zaben shugaban kasa yana tafe a badi.