✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba ta yin abin da ya dace wajen rage yawan haihuwa – Hukumar Kidaya

Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Nasir Isah Kwarra, ya ce Najeriya ba ta yin abubuwan da suka kamata wajen kayyade yawan haihuwa kamar yadda aka…

Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Nasir Isah Kwarra, ya ce Najeriya ba ta yin abubuwan da suka kamata wajen kayyade yawan haihuwa kamar yadda aka tsara.

Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata, lokacin da yake jawabi a yayin Taron Kasa da Kasa kan Yawan Jama’a (ICPD) a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Shugaban ya ce rashin samar wa da hukumar tasa isassun kudaden gudanarwa a kasafin kudi ne babban tarnakin da shirin ke fuskanta.

Nasir Kwarra ya kuma ce, “Idan zan fada muku gaskiya, ba mu yi abin da ya dace ba a wannan bangaren. Akwai bukatar gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen ganin an lalubo bakin zaren.

“Matukar ba mu tashi tsaye mun yi wadannan abubuwan ba, ban san ta yadda za mu kayyade yawan jama’a ba a Najeriya.

“A yanayin yawanmu a yanzu, muna bukatar nagartaccen tsarin tattalin arzikin da zai yi daidai da yawan jama’armu, muddin ba mu yi haka ba kuma, za a ci gaba da fuskantar matsalar karancin abinci, musamman a tsakanin matasa, wadanda su ne suka fi yawa a Najeriya,” inji shi.

Ya kuma lura cewa har yanzu Najeriya na kan gaba a jerin kasashen da ba sa iya samar da abubuwan da matan aure suke bukata na kayyade iyali, inda take da kaso kusan 19 cikin 100.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa hukumarsa isassun kudaden da za ta yi amfani da su wajen samar da kayan tsara iyali.