Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce Najeriya ba ta taba samun shugaba kasa mai nagartar Muhammadu Buhari ba.
Masari ya ce tun da turawan mulkin mallaka suka hade Kudanci da Arewacin Najeriya a shekarar 1914, Najeriya ba ta taba dacen shugaba nagari kamar Buhari ba.
- PDP na taro kan yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa
- An daure Mubarak Bala shekara 24 kan aikata sabo
Ya yi wannan furuci ne a yayin da ya ke jawabi a gaban wani gangamin cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na tabbatar da daidaito a wajen rabon albarkatun kasa ranar Asabar a Katsina.
Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da suke shan matsin lamba daga hare-haren ‘yan bindiga da satar shanu.
Sakamakon kamarin da matsalar ta yi ne ma, wani lokaci a baya gwamna Masari ya ce lamarin ya fi karfin hukumomin tsaron kasar nan, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su dauki makami don kare kansu.
Dubban mutane ne dai ‘yan bindiga suka kashe, ko suka sace su don karbar kudin fansa a Katsina da sauran jihohin arewa irin su Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Kaduna, Neja da sauransu.