Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta ce Najeriya ba ta da wani dakin gwaje-gwaje ko daya da zai haifar da cutar kyandar biri.
Babban Daraktan Hukumar, Ifedayo Adetifa ne ya bayyana hakan a martaninsa ga wani rahoto na Shugaban Kula da Sinadarai da Tabbatar da Kare Ilimin Halittu na Kasar Rasha.
- NECO: Dalibai sun shiga zullumi bayan Ganduje ya tsaurara sharadin daukar nauyin jarabawa
- Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindiga a hanyar Birnin Gwari
Rahoton shugaban za yi zargin akwai dakunan gwaje-gwaje da nazarin halittu har guda hudu da ke aiki a Najeriya.
Haka zalika ita ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta rawaito cewa kwayar cutar Kyandar Birin da ta bulla a nahiyar Turai da wasu sassan duniya ta fito ne daga Najeriya, in da kasar Amurka ta tura kayan more rayuwar halittu.
Abinda NCDC ke cewa kan Zargin Rashan
Sai dai Ifedayo ya ce babu wata shaida da Rashan ke da ita da zai tabbatar da zargin.
“Ayyukan Najeriya a dakunan gwaje-gwajen Lafiya sanannu ne ga hukumomi masu sanya ido, kuma yawancinsu Gwannatin Tarayya ce ta samar da su a jihohi 36 da kuma Abuja.
“Ta samar da su ne domin gwajin cutuka, musamman cutar COVID-19, da sauran cututtuka masu yaduwa” in ji shi.
Daraktan ya ci gaba da cewa: “Wasu dakunan gwajin kuma an bar su domin cutar HIV, wanda Gwamnatin Tarayya ce da abokan huldarta a bangaren lafiya, da kuma NCDC ke kula da su.
Alakar Najeriya da Kasashen Turai a bangaren kimiyya
A don haka Daraktan ya ce bisa tsari, Najeriya na maraba da da dukkanin hadin gwiwa a bangaren kimiyya, kuma ta samu tallafi da dama daga kasashen Birtaniya da Jamus da Japan da sauransu.
Kazalika Ifedayo ya ce Najeriyar na tattaunawa da Rasha domin fara hada rigakafin cututtuka a kasar.