More Podcasts
Bayanin rage adadin kwanakin zuwa makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a wannan zango ya dauki hankalin malaman makarantu da masana harkar ilimi a Jihar.
Malaman makaranta na ganin cewa tsarin da zai tilasta wa makarantu hutun kwana uku a sati zai kara takure su wurin shirya jadawalin darussan da za su koyar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da tattaunawa ta musamman da Malamai da masana harkokin ilimi akan wannan batu.