✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: ’Yan Kudu sun mayar da mu abin kashewa a yankinsu —’Yan Arewa

’Yan Arewacin Najeriya sun ce, “Ana tsangwamar mu da kyamar mu, har ma da kashe mu a Jihar Anambra.”

More Podcasts

Domin sauke Shirin latsa nan.

’Yan Najeriya na yi wa kasarsu kirari da cewa ‘kasa daya, al’umma daya’.

Amma ’yan Arewacin kasar mazauna yankin Kudu sun koka bisa yadda suka yi zargin an mayar da su abin kashewa da kuma tsangwama a yankin da suke zama.

Shin ina ’yancin da tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasar na zama a duk inda yake so a bisa doka, ba tare da an cutar da shi ko an nuna masa wariya ba?

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wasu ’yan Arewa mazauna Jihar Anambra kan yadda suke rayuwa a can.