More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Hukumomin tsara birane a Najeriya sukan yi rusau a wuraren da hakan ta kama a yayin gudanar da ayyukansu.
Duk lokacin da hukumomin suka tashi jama’a daga inda suke gudanar da harkokin ko gidajensu, lamarin kan jefa mutanen da hakan ta shafa cikin gigicewa.
Wasu daga cikin mutanen na zargin cewa hukumomin na zaluntar masu karamin karfi ne kawai.
Shin hukumomin na sanar da jama’ar da lamarin ya shafa kafin a rushe kadarorinsu?