More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Dabi’ar daukar doka da mutane ke yi a hannunsu ta hanyar kama mai laifi, sannan kafin a yi bincike su dauki hukunci ta hanyar duka, sara ko saka wa mutum taya a wuya a zuba fetur a cinna wuta, na dada karuwa a tsakanin mutane a ’yan kwanakin nan.
Rahotanni na yawan fitowa daga yankunan Kudu maso Yammaci da Arewa maso Yammacin Najeriya kan hukuncin na daukar doka a hannu.
Me yasa hakan ke yawan faruwa?
Ina mahukuntan kasar suke da har rai ke neman zama ba a bakin komai ba?