Domin sauke shirin latsa
Mene ne kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan wanda aka fusata shi ya dauki doka a hannunsa?
Tun bayan abin da ya faru na zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a Sakkwato da daukar matakin da matasan Musulmi suka yi na halaka wacce ta yi batancin nan take, jama’a ke ta musayar ra’ayi kan matsayin shari’a kan wannan batu.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Kawar da ’Yan Fadar Buhari
- DAGA LARABA: Dalilin Da Muka Bar Matasan Arewa A Baya.
Wakilinmu a Jihar Sakkwato ya fada mana halin da jihar ke ciki, mun kuma ji ta bakin wani mai fashin baki kan dokokin kasa kan abin da ya faru.