A Talatar da gabata ce kotu ta tabbatar da tuhume-tuhume uku da ake yi wa Derek Chauvin, tsohon jami’in dan sandan Amurka da aka zarga da yi wa wani bakar fata kisan ganganci kusan watanni 10 da suka gabata.
A yanzu dai Mista Chavin yana fuskantar hukuncin cin sarka a gidan Dan Kande na tsawon shekara arba’in a kan laifin kisa mataki na biyu, da daurin shekara na kisan kai mataki na uku, da kuma wasu shekaru goma kan kisan ganganci.
- ‘Babu wanda cutar Coronavirus ta kashe tsawon kwana tara a Najeriya’
- ’Yan awaren Biyafara sun kai wa Fulani hari a Imo
Bayan Alkalan kotun sun tattauna na tsawon sa’a 11, sun tabbatar da dukkan tuhume-tuhume uku da ake yi wa Mista Chauvin mai shekara 45, lamarin da share hawayen masu ganin ’yan sanda na wuce gona da irin yayin gudanar da ayyukansu a Amurka.
Yayin zaman kotu, daruruwan mutane suka taru a harabarta da ke Minneapolis wacce ke zagaye da jami’an tsaro, inda suka bayyana farin cikinsu kan hukuncin da kotun ta yanke bayan an kwashe tsawon makonni uku ana shari’a.
Nan take jami’an tsaro suka daure shi da ankwa bayan alkalin gundunmar Hennepin, Peter Cahil ya karanta hukuncin, wanda dukkan alkalai biyar na kotun suke amince, sanna aka fice da shi daga kotun yana sanye da takunkumin rufe fuska ba tare da ya nuna wata alamar damuwa a tattare da shi ba.
A ranar 24 ga watan Mayun bara ce, George Floyd ya riga mu gidan gaskita bayan Mista Chauvin ya yi durkuson gwiwa a wuyansa yayin da ya kama shi a matsayin wanda ake zargi da siyan kaya a wani shago da takardar kudin jabu ta dala 20.
An yi ta yayata hoton bidiyon wannan durkoso da gwiwar kafa da Mista Chauvin ya yi a kan wuyan marigayi Floyd da ke kwance rub da ciki har na tsawon minti tara da rabi, alhali yana daure da ankwa, kuma yana da kakarin bayan iya numfashi.
Babu shakka har kawo yanzu, mutuwar Floyd ta janyo zanga-zanga a duk fadin duniya, inda ake ta nuna kin jinin cin zarafin mutane musamman bakar fata da jami’an tsaro ke yi.
Ana iya tuna cewa, sai bayan watanni tara da mutuwar George Floyd ne aka fara shirin gurfanar da Mista Chauvin da ake zargin ya yi ajalinsa a gaban kuliya, inda a ranar 29 aka fara fafata shari’a kuma aka samu kammalallen hukuncin kan lamarin a yanzu.