More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Shirin Najeriya A Yau ya yi tattaunawa ta musannan da Malam Tukur Manu kan yadda ya sayar da ransa wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna daga hannun ’yan ta’adda.
A ranar Babban Sallar nan ce Tukur Mamu ya je har maboyar ’yan bindigar suka sako mutum bakwai daga cikin fasinjojin — kari a kan 11 da suka saki a watan jiya.
NAJERIYA A YAU: Haduwar Ranakun Arafa Da Juma’a A Hajjin Bana
Zaman lafiya zai dawo Najeriya kafin Buhari ya bar mulki — Malami
Wasu a cikinsu sai da aka biya fansa aka sake su, wasu kuma haka nan ’yan ta’addan suka sake su.
Fiye da wata uku ke nan bayan ’yan ta’adda sun yi garkuwa da fasinjoji 62 a harin da suka kai wa wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris na bana.
To sai dai har yanzu suna rike da ragowar fasinjojin, suna jira gwamnati ta biya wasu bukatunsu cikin har da sakin wasu daga cikin ’yan uwansu kafin su sako sauran fasinjojin.
Tun a watan Yunin ne dai wani mai suna Malam Tukur Mamu ya rika fadi-tashin shiga tsakani, da yin sulhu wajen ganin ’yan ta’addan sun sako fasinjojin.
Ga yadda tattaunawar shirin Najeriya A Yau ta kasance mai shiga tsakanin.