✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Haddasa Dambarwar Sarauta A Kano

Gwamna Abba ya sanya hannu kan dokar da ta soke sabbin masarautun da Ganduje ya kirkira shekara hudu baya.

More Podcasts

A ‘yan shekarun da suka gabata tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka da ta karkasa Masarautar Kano gida biyar, daga bisani kuma ya tsige sarkin Kano na 14 bisa zargin aikata ba daidai ba da rashin da’a.

Yanzu shekaru hudu bayan hakan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata dokar da ta soke wadancan matakan da kuma sake tabbatar da Muhammadu Sanusi kan matsayinsa na Sarkin Kano.

Shin mene ne ya bambanta wancan lokacin da yanzu; me ya sa ake ta dambarwa har yanzu?

Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan dambarwar cire Sarakunan Kano tun daga tushe.

Domin sauke shirin, latsa nan