✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: ‘Illolin kaurace wa zabe sun fi na kada kuri’a yawa’

Domin sauke shirin latsa nan Bayan ya dade yana jan hankalin hukumomi game da bukatar daukar mataki a kan rashin tsaron da ya gallabi ’an…

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Bayan ya dade yana jan hankalin hukumomi game da bukatar daukar mataki a kan rashin tsaron da ya gallabi ’an Najeriya, wani limami ya yi kashedin cewa mutane ba za su fito zabe ba a 2023 idan ba a amsa wasu tambayoyi ba.

Da jin haka, kwamitin masallacin da Sheikh Nuru Khalid yake jan sallar Juma’a ya ce malamin ya wuce gona da iri, yana tunzura mutane kada su fito zabe.

Shirin Najeriya a Yau zai duba ya gani, ko kin fita zabe ne zai magance wannan matsala ko akwai wata mafitar.