More Podcasts
Yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake gabatar da Ƙudurin Kasafin Kuɗi na 2025, shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ɗauke hankalin jama’a ya yi da sanar da tsawaita wa’adin Kasafi na bana zuwa tsakiyar baɗi.
Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa wannan lamari ka iya haifar da rikita-rikita a fannin tattalin arziki da ma wasu ɓangarorin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tamowa Ke Kassara Yara a Katsina
- DAGA LARABA: Me nasarar John Mahama ke nufi ga ƙasar Ghana?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda aiwatar da kasafin kuɗin bara da na bana a lokaci guda zai shafi rayuwar ’yan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan