✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: Dole A Gwada Kwarewarsu Kafin A Ba Su Aiki —Tilde

Rashin daukar wadanda Gwamnatin Jihar Bauchi da UNICEF suka tura karatun NCE aikin koyarwa a jihar ya bar baya da kura

More Podcasts

Domin sauke shirin domin sauraro a duk lokacin da kuke so, latsa nan

Wadansu mutane da Hukumar UNICEF da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi suka dauki nauyin karatunsu a fannin koyarwa bisa sharadin gwamnatin jihar za ta dauke su aiki a makarantunta bayan an yaye su, na zargin gwamnatin jihar da yin watsi da alkawarin da ta yi musu a lokacin tura su karatu.

To ko ya aka yi labari ya sha bambam a kan daukar malaman?

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da bangarorin da abin ya shafa dama Gwamnatin Jihar Bauchi domin gano bakin zaren.