More Podcasts
Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su.
Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana.
An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara.
- NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu
- DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance Tamowa a wasu jihohin Arewa maso Gabas.
Domin sauke shirin, latsa nan