More Podcasts
Gurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.
Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, waɗanda wasu suke cewa ƙanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dawo Da Wutar Lantarki Zai Sauya Arewa
- DAGA LARABA: Adawar Gwamnonin Arewa da Ƙudurin Haraji: Kishin Ƙasa Ko Son Zuciya?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan tanadin doka game da kamen ƙananan yara da kulle su da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
Domin sauke shirin, latsa nan