More Podcasts
Tun kafin sanar da sabuwar ƙawance da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yi wa wannan haɗaka zagon ƙasa da kawo cikas ga tafiyar.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan zagon ƙasa da ake zargin wasu da yi wa wannan sabuwar haɗaka, ita ce na sanar da su rashin samun ɗakin taron da suka shirya gudanar da taron lokaci ƙalilan gabanin taron.
- NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya
- DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan noyayyun ƙalubalen da sabon haɗakar jam’iyyar ADC za ta iya fuskanta gabanin 2027.
Domin sauke shirin, latsa nan