✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naira miliyan 15 kacal Hukumar JAMB ta baiwa Gwamnati -Bincike

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano Hukumar da ke Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a ta (JAMB) ta samu fiye da Naira biliyan…

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano Hukumar da ke Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a ta (JAMB) ta samu fiye da Naira biliyan 30 cikin shekaru biyar amma kimanin Naira miliyan 15 ta baiwa Gwamnatin Tarayya.
Hukumar JAMB din ta samu kudin daga kudin rajistar da dalibai suka biya wadanda suka zana jarabawar share fagen shiga jami’a tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Dalibai fiye da miliyan bakwai ne suka zauna jarabawar a cikin shekaru biyar inda suka biya tsakanin Naira dubu hudu zuwa Naira dubu hudu da 600 na kudin rajista.
Mako biyu da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta bayar da ummarnin a binciki tsofaffin shugabannin hukumar JAMB din tare da wadansu hukumomin gwamnati da ba su baiwa gwamnati kudin shigar a-zo-a-gani ba.