Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Suleiman Adamu ya ce Ma’aikatar Ruwa na bukatar Naira biliyan 26 wajen ganin an magance karancin ruwa a kasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen kare kasafin kudin ma’aikatar na badi a gaban Kwamitin Albarkatun Ruwa na Majalisar Dattawa.
- Kwalara ta kashe ’yan gudun hijira 23 a Kamaru
- Dan asalin Indiya na daf da zama Firai Ministan Birtaniya
Injiniya Suleiman Adamu ya ce ma’aikatarsa ta bullo da wasu dabaru da za su taimaka wa kasa wajen samun wadattacen ruwa na noma, walau na ayyukan tafiyar da ruyuwa na yau da kullum, har da ma na noman rani.
Ya ce ba aikin Gwamnatin Tarayyya ba ne samar da ruwa a jihohi amma tana iya ba jihohin tallafi domin su samu wadattacen ruwa.
Ministan ya kara da cewa, akwai wata doka ta ruwa da ke gaban Majalisar Tarayya, wanda idan an kammala aiki akan dokar zai inganta hanyoyi na gudanar da ayyukan albarkatun ruwa a kasar.
Haka su ma manazarta na ganin samar da wadataccen ruwa ba aikin Gwamnatin Taraiyya ba ne.
Wannan matsala ta ruwa ta haifar da bullo da amfani da ruwan gora ko roba ko ruwan leda wanda aka fi sani da pure water a turanci.
A hirar shi da Muryar Amurka, manazarci a siyasar tattalin arziki da ci gaban kasa, Nasiru Marmara ya bayyana hangensa kan aikin ma’aikatar ruwa ta tarayya da jihohi.
Ya sanar cewa yana ganin wannan fanin ya dan samu matsala a Najeriya saboda wasu dalilai da suka hada da cewa ba ko’ina ba ne ake samun wadataccen ruwa, domin mahukunta basu kula da madatsun ruwa ba, ko kuma an bar su sun lalace.
Nasiru ya ce ba a fadada hanyoyin samun ruwan famfo ba, saboda a yanzu an samu karuwa na mutane a ko’ina.
A nashi bayanin, Ibrahim Jalo yana ganin bai kamata Gwamnatin Tarayya ta zama mai daukan nauyin samar da ruwa a kasa ita kadai ba.
Ya bayyana cewa yana ganin kananan hukumomi ne ke da alhakin samar da wadattacen ruwa ga al’umma, amma matsalar ta kara tsananta ne domin gwamnoni sun yi wa ayyukan kananan hukumomi katsalandan.
Bisa ga cewarsa, sun mayar da kananan hukumomi wani bangare na gidajensu, saboda haka ba sa aiki yadda ya kamata.