✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu na N2bn a Kano da Anambra

Babbar Daraktar ta kuma ce sauran kayayyakin sun hada da kwayoyi da magungunan hawan jini da na zazzabin cizon sauro da kuma na kara kuzari.

Kwayoyi, allurai, kayan kwalliya da kayan abincin da suka lalace wadanda kimarsu ta kai kimanin Naira biyu ne Hukumar Kula da Lafiyar Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta lalata a jihohin Kano da Anambra.

Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi ta ce ta dauki matakin lalata kayayyakin ne da nufin kakkabe jabun magunguna da sauran kayan abincin da ba su da inganci a Najeriya.

Kayayyakin dai na sama da Naira biliyan daya da miliyan 400 da aka kwace daga sassa da dama na jihohin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ne aka lalata a birnin Awka na jihar Anambra ranar Alhamis, yayin da aka lalata na sama da Naira miliyan 613 a garin Kalebawa da ke Karamar Hukumar Danbatta a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an hukumar sun shiga lungu da sakon shiyyoyi uku ne na Arewa maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu wajen zakulo jabun kayayyakin kafin ta kai ga lalata su.

Babbar Daraktar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye wacce ta jagoranci lalatawar ta ce kayayyakin sun hada da abinci da magunguna da kayan kwalliya mara sa inganci da kuma na jabu daga masu sarrafawa, masu rarrabawa da kuma masu shigo da su.

Ta ce kamfanonin da suke korafi, kungiyoyi masu zaman kansu da na ’yan kasuwa, Kungiyar Masana Kimiyyar Harhada Magunguna ta Najeriya (PSN) da Kungiyar Dillalan Magunguna ta Kasa (NAPPMED) ne suka mika kayayyakin ga hukumar.

Farfesa Mojisola ta kuma ce daga cikin kayayyakin akwai wadanda Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa ta kwace saboda karya dokokin fito, ciki har da kwayar maganin Tramadol.

Babbar Daraktar ta kuma ce sauran kayayyakin sun hada da kwayoyi da magungunan hawan jini da na zazzabin cizon sauro da kuma na kara kuzari.