Hukumar NAFDAC mai kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya, ta karrama mukaddashin Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano (KCPC), Baffa Babba Dan Agundi saboda kokarin da yake na yaki da jabun magunguna a jihar.
Daraktan NAFDAC reshen Jihar Kano, Pharm. Shaba Muhammad ne ya gabatar da lambar yabo ga Babba Dan Agundi yayin da ya kai ziyarar aiki ofishin Hukumar NAFDAC a ranar Talata.
- An yi zanga-zanga kan yunkurin mayar da mafi karancin albashi hannun Gwamnoni a Kano
- Kotu ta tsare wanda ya yi wa yarinya mai shekara 10 fyade
- Ya saki matarsa saboda ta fiye zafin rai
Pharm. Shaba ya ce NAFDAC ta yaba da kokarin Baffa Babba wajen yaki da samarwa da sayar jabun magunguna a jihar Kano wanda ya samu gagarumar nasara cikin kankanin lokaci tun bayan zamansa mukaddashin hukumar KCPC.
Ya kara da cewa, NAFDAC za ta hannu da Hukumar KCPC domin inganta ayyukan tsabtace jihar Kano daga samarwa, fasa kwauri da kuma sayar da magungunan jabu a cikin jihar.
“Idan muka hannu tare za mu iya tsaftace Kano kuma idan muka tsaftace Kano mun tsaftace Najeriya,” in ji Pharm. Shaba.
A nasa jawaban, Baffa Babba wanda ke zaman Shugaban Hukumar KAROTA mai kula da zirga-zirgar ababen hawa a Jihar Kano, ya ce ya ziyarci ofishin NAFDAC ne domin neman hadin kansu wajen yaki da jabun magunguna da kuma miyagun kwayoyi a jihar.
Ya ce Hukumar KCPC da yake jagoranta ta dukufa ne wajen lalubo wadanda ke harkar samarwa da sayar da jabun magunguna a jihar,
Sannan ya yi kira ga Hukumar NAFDAC a kan ta inganta hanyoyin da za su kawo saukin yi wa kayayyakin abinci da magunguna rajista ba tare da daukar wani lokaci mai tsawo ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, wakilan kungiyar masu sayar da magunguna a jihar Kano suna cikin ’yan tawagar da ta yi rakiyar mukaddashin KCPC zuwa ofishin na NAFDAC.