Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta gano wani waje a Jihar Abiya da ake sake gyara da sabunta magungunan da suka lalace domin sayar wa jama’a.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.
- Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro
- Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki
Hukumar ta ce an gano waɗannan magunguna a wasu gine-gine da ke garin Umumeje, a Ƙaramar Hukumar Osisioma Ngwa.
NAFDAC, ta ce wannan waje yana kusa da kasuwar Ariaria a Aba, cibiyar kasuwanci a jihar.
Hukumar ta bayyana cewa ta kai samame wajen ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin daƙile safarar jabun magunguna.
Wannan yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na kare lafiyar al’umma.