✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Hukumar ta ce dole ne al'umma su zama masu sanya ido wajen kare kayayyakin da ke samar da wutar lantarki.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), ta bayyana cewa an lalata manyan turakun wutar lantarki sama da 18 a jihohin Ribas, Abiya, da Kano tsakanin ranakun 9 zuwa 14 ga watan Janairu, 2025.

A Jihar Ribas, an lalata turakun wutar lantarki da ke kan layin Owerri/Ahoada 132kV, yayin da a Abiya aka sace wasu manyan wayoyi da wasu sassan gine-gine na turakun da ake yi wa gyare-gyare.

Haka kuma, a Kano, ɓata-gari sun lalata turakun da ke kan layin Katsina zuwa Gazoua mai nauyin 132/33kV.

Hakazalika, a Abuja, an gano an lalata wayoyin da ke ƙarƙashin ƙasa na wutar lantarki a ranar 17 ga watan Janairu, wanda ya kawo tsaikon ɗauke wutar lantarki a yankunan birnin.

Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ta bayyana wannan matsalar a matsayin babbar barazana ga ci gaban wutar lantarki.

Ta roƙi al’umma da su taimaka wajen kare waɗannan kayayyaki domin amfanin kansu da gwamnati.

Ta jaddada cewa hanyoyin wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa, don haka kowa ya taimaka wajen magance wannan matsala.