✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta kama ganda mai dauke da guba ta N23m a Legas

An yi kiyasin farashin gandar kan kusan naira miliyan 23.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta kama tan 120 na wata ganda da ake zargi tana dauke da sinadarai masu hadari ga lafiya wadda aka shigo da ita kasar.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa an kama gandar mai tarin yawwa wadda ake zargi tana da hadari ga lafiya a wurare shida a Legas.

Shugabar Hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa mutum bakwai da ake zargi da wannan lamarin ana gudanar da bincike a kansu.

Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa tuni aka dauki samfurin gandar domin kai ta dakin gwaji domin gano ingancinta, inda take gargadin ’yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan wajen sayen ganda.

Ta kuma bayyana cewa an yi kiyasin farashin gandar kan kusan naira miliyan 23.

Tana mai cewa Hukumar NAFDAC tana shawartar ma’abota cin ganda da sauran masu cin kasuwarta da su guji sayen duk wata fatar dabba a matsayin abin ci.

Ta ce ana amfani da sunadarai masu hadari ga lafiya wajen sarrafa wannan ganda kuma galibi tana da hadarin gaske ga lafiyar al’umma.

Ta kara da cewa, cin irin wannan ganda na iya janyo lalacewar koda, hanta da kuma zuciya, kari a kan wasu cututtuka masu nasaba da sankarar jini da sauran dangin cututtukan daji.

A kan haka ne Farfesa Adeyeye take shawartar yan kasar da su bude idanunsu sosai wajen sayen duk wata ganda da sauran kayayyakin abinci.