✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC Ta Haramta Amfani Da Sabulun Dex Luxury

NAFDAC ta ce sabulun na dauke da sinadarin da ke illa ga kwayoyin halittar dan Adam da kuma yaran da ke ciki

Hukumar Kula da Abinci Ingancin da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta haramta amfani sabulun Dex Luxury saboda illarsa ga lafiyar dan Adam.

NAFDAC ta bayyana cewa sabulun na Dex Luxury na dauke da sinadarin butylphenyl methylpropional, wanda da ke illa ga yaran da ke ciki da kuma kwayoyin halittar dan Adam.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar 14 ga watan Afrilu a shafinta na X, inda ta ce ta haramta amfani da sayar da wannan sabulu a fadin Najeriya.

Ta kara da cewa ta dakatar da Sabulun Dex Luxury Bar (No 6 Mystic Flower) kamar yadda  Tarayyar Turai (EU) ta haramta.

EU ta bayyaa cewa sabulun, wanda ake yi a kasar Turkiyya, na dauke da BMHCA, wani sinadari da aka haramta amfani da shi a cikin kayan kwalliya, saboda yana iya janyo cutarwa ga fata da kuma tsarin haihuwa.

NAFDAC ta ce a yanzu haka wannan sabulu baya cikin jerin kayyakin da ta sahalle a shigo da su Najeriya.

Amma duk da haka, tun da akwai rahotanni kan sayar da samfurin sabulu a wasu shaguna a kasar, ta haramta sayarwa ko amfani da shi.