✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta gargadi ’yan Najeriya kan cin kajin da aka yi fasa-kwaurinsu

Hukumar ta ce kajin na dauke da sinadarin formalin mai dauke da guba.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gargadi ’yan Najeriya kan cin kajin da aka yi fasa-kwaurinsu, musamman wadanda suka jima a cikin kankara.

Kakakin hukumar, Abubakar Jimoh ne ya yi gargadin yayin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Jimoh ya ce irin wadannan kayan abincin wadanda ake amfani da sinadarin formalin na dauke da guba wacce take da illa ga lafiyar mutane.

Ana dai amfani da sinadarin formalin ne wajen adana gawarwaki a dakunan ajiye su.

“NAFDAC na gargadin ’yan Najeriya kan ta’ammali da irin wadannan kajin. Muna da wadatattun kaji a kasarmu da ba sai mun yi amfani da irin wadannan masu illar da aka yi fasa-kwaurinsu, duk kuwa da cewa gwamnati ta hana yin hakan,” inji shi.

Ya ce muddin ba a kiyayi fasa-kwaurin ba, hakan zai yi mummunar illa ga masu kiwo da ma kasuwancin kajin na cikin gida.