Hukumar Kula da Ingancin Magunguna da Kayan Abinci a Najeriya (NAFDAC) ta yi kira da a kaurace wa wasu nau’ukan magungunan tari wadanda ake alakanta su da mutuwar yara da dama a Kasar Gambiya.
Ana zargin cewa magungunan iri hudu, na kamfanin hada magani na Maiden Pharmaceuticals da ke Indiya, sun gurbata ne da wasu abubuwa masu cutarwa.
- Dan shekara 5 ya mutu a motar makaranta a Saudiyya
- Akwai kamanceceniya tsakanin Masarautar Kano da ta Ingila —Nasir Khalil
A cikin wata sanarwa da NAFDAC ta fitar, ta ce duk wanda ya san ya yi amfani da wani daga cikin irin wadannan magunguna, kuma ya ji wasu alamomi da bai gane ba a tare da shi, to ya garzaya ya sanar da hukumomin lafiya.
Hukumar ta kara da cewa wasu daga cikin cututtukan da magungunan ke haifarwa sun hada da ciwon ciki, da amai, da gudawa, da gaza yin fitsari, da ciwon kai, da lalurar koda mai tsanani wadda ka iya sanadin mutuwa.
Sai dai sanarwar ba ta fayyace ko akwai magungunan a kasuwannin Najeriya ba.
Kazalika, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargadi kasashen duniya kan su yi hattara da magungunan na yara.
Magungunan tarin dai su ne na ‘Promethazine Oral Solution’, da ‘Kofexmalin Baby Cough Syrup’, da ‘Makoff Baby Cough Syrup’ da kuma ‘Magrip N Cold Syrup’.
A wata sanarwa da kamfanin magungunan ya fitar, ta ce ya yi takaicin matsalolin da magungunan suka haifar.
Kamfanin ya kara da cewa ya bi duk wasu ka’idojin da aka gindaya na hada magani a kasar Indiya, kuma yana bayar da hadin kai a binciken da ake gudanarwa.
Tuni dai Gambia ta fara janye magungunan daga kasuwanninta, inda ake alakanta magungunan tarin da yin sanadin mutuwar akalla yara 69.
Kuma hukumar lafiya ta nuna fargabar cewa ba a Gambia kawai ake amfani da magungunan ba.