✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi nadamar shiga siyasa – Tsohon Shugaban Majalisa

Alhaji Inuwa Garba matashi ne kuma shi ne tsohon Shugaban Majalisar dokokin jihar Gombe wanda da ya fi karancin shekaru a fadin Najeriya a lokacin.…

Alhaji Inuwa Garba matashi ne kuma shi ne tsohon Shugaban Majalisar dokokin jihar Gombe wanda da ya fi karancin shekaru a fadin Najeriya a lokacin.

Aminiya: Yaya aka yi ka shiga siyasa duk da kana da karancin shekaru?
 Sunana Honorabul Inuwa Garba, tsohon dan majalisar dokokin jihar Gombe mafi karancin shekaru, na zama mataimakin shugaban majalisa mafi karancin shekaru, sanna na zama shugaba mafi karancin shekaru. Da kuma likkafa ta yi gaba aka zabe ni a matsayin shugaban ko Jagoran dukkannin shugabannin majalisun jihohin kasar nan. Watau na gaji tsohon shugaban majalisan dokoki ta jihar Ribas Rotimi Ameachi. Kuma a yanzu ina rike da mukamin mataimaki na musamman ga mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ikweremadu. Na shiga siya ne don in taimaka wajen tallafawa don gina kasa ta Najeriya da Jiha ta ta Gombe da kuma mazabata.
 Aminiya: A matsayinka na dan siyasa, kuma tsohon dan majalisa, wace shawara za ka ba ‘yan siyasa a yanzu?
 Ya kamata su fahimce aikinsu don sune muryar talakawa. Su ke bin diddigi don ganin an yi wa jama’a aiki ta hanyar tattaunawa d a yi wa dokoki garanbawul da kuma duba ayyuka don ganin abin da aka rubuta an bi shi sau da kafa ba a yi rub da ciki da kudin jama’a ba. Kuma ana haka ne don bangaren zartarwa ya yi aikinsa da inganci.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da jinkirin da aka samu daga ‘yan majalisun tarayya kafin aka rattaba hannu a kasafin kudi. Shin ba a cutar da talaka ba kuwa?
 Duk abin da ya faru ya faru ne saboda siyasa. Domin ‘yan majalisa suna son ganin an bi tsarin dimokradiya kamar yadda doka ta yi tanaji. Don an zabe su ne domin su bi diddigin abin da aka kawo gabansu don su yi mahawara a kai. Domin akwai kudurin da ake neman samun akalla mambobi kashi biyu bisa uku kafin a aminice da shi, wani kuma yana neman rinjaye ne ko na kuri’a daya ne. Sannan idan ba jama’a akalla kashi biyu bisa uku, to ba a yin zama sam-sam. Watau mutum hudu ko biyar ba za su zauna su ce sun zartar da wani kudiri ba. A matsayina na dan siyasa bangaren majalisa, ina ba su shawara da su kara zage damtse domin ciyar da kasa gaba.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da ‘yan siyasa masu tsalle daga wannan jam’iya zuwa wata?
 Na yi siyasi cikin PDP, kuma ina cikinta har yanzu tsundum. Ban sauya jam’iya ba duk da ina matashi, amma sai ga shi wadansu manya suna nuna halin rashin jajircewa a wuri guda, sun koma suna harshen damo. Duk da dai duk jam’iyun suna da burin ganin an ciyar da kasa gaba ne. Lallai ba a siyasa sai da zaman lafiya. Sannan akwai ‘yan siyasan yunwa wadanda a kullum su ‘yan neman a ci bulus ne. ‘Yan yunwa a PDP sun koma APC don a kayar da PDP, sannan suna ta kurarin canji, to an samu mulki, amma har yanzu ba a gani a kasa ba. Don an dauki shekara daya kafin aka sa hannu a kasafin kudi. Kowa ya san dai an yi latti. APC ba su iya mulki ba sam-sam. In da sun iya mulki, da yanzu an ga sauyi tun daga ranar da suka hau mulki. A ganina an dai sauya suna ne daga PDP zuwa APC.
Aminiya: Yaya za a yi a warware matsalolin da PDP ta fada ciki tsundum?
Ai sai an samu matsala sannan ake warware ta. Kuma an kusa shawo kan al’amarin, nan ba da dadewa ba.
Aminiya: Shin ko ka yi nadamar shiga siyasa?
 kwarai da gaske na yi nadamar shiga siyasa. Dalilin kuwa shine, ba ka iya wa, ba a yaba ma, ba ka gamawa, ba ka barin siyasa. Don mutane so suke ka burge su, Kai kuma dan majalisa dole ne ka tuntubi abokan aiki don a aminice da kudurin da ka gabatar. Daga nan za a nemi masana su ga aikin da neman yardar bangaren zartarwa da ma’aikata game da tsarin aiki da bin lauyoyi don a bi doka. To idan ba ka hada kai da saura ba, ba abin da za a yi, Amma wadansu so suke da ka shiga ofis yau a maida komai sabo a ranar, wanda ba haka tsarin yake a mulkin siyasa ba. ‘Yan siyasa ba su saurin fahimtar uzurinka, musammam ma wadanda kuka yi yawon neman zabe tare. Kowa so yake ka gan shi, ka ji shi, wanda ba haka ba ne. Nanmajalisar mazabata lokacin ina makarantar firamare har na kai ga haka, shi ma har yanzu bai bar siyasa ba. Don haka ni ma na sa talalmin-kaza ke nan, don idan an shiga siyasa ba a fita, don haka ni ba zan iya fita ba. Ina shawartar ‘yan siyasa da su dage don gina kasa. Sannan duk gwamnati tana da nufin alheri, sai dai a samu akasi. Ina kira ga jama’a da su rika yi wa shugabanni addu’a ta kwarai, sannan a rka biyan haraji domin a tallafa don gina kasa. A da magabatanmu sun biya haraji, don haka mu ma mu yi koyi da su.
Aminiya: Kana da shekara nawa ka zama dan majalisa?
 Ba zan fadi ba. (Dariya).