✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi murna ’yan Najeriya sun koma gona — Buhari

Tsohon shugaban ya ce noma abinci a cikin gida zai rage hauhawar farashin kayan abinci.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin daɗinsa kan yadda al’ummar ƙasar nan da yawa suka koma gona domin samar wa kansu abinci.

Buhari ya ce noma kayan abinci a cikin gida, zai taimaka matuƙa wajen rage hauhawar farashin kayan abinci.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda al’ummar ƙasar nan ke haihuwa barkatai.

A gefe guda, kuma ya jaddada buƙatar tattaunawa, wayar da kan jama’a, da saka hannun jari a fannin ilimi da lafiya don magance wannan matsala.

Ya bayyana hakan ne a fadar Sarkin Daura bayan idar da Sallar Idi, inda taya ɗaukacin ’yan Najeriya murnar bikin sallah babba tare da yi musu addu’ar samun wadata da lafiya.

Ya bukaci ’yan ƙasar nan da su koma noma abincinsu da kuma tallafawa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida don bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya bayyana irin gudummawar da gwamnatocin baya suka bayar wajen aza harsashin samar da al’umma mai wadata.

Buhari ya yi kira ga matasa da su yi koyi da iyayen da suka kafa ƙasa wajen gina Najeriya.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da su tallafa wa juna kuma su kasance masu kula da ’yan’uwansu, musamman a lokutan da ake fuskantar matsin rayuwa.

Da yake jawabi ga matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Buhari ya yaba da shirin, inda ya bayyana shi a matsayin hanya da haɗa kan ’yan kasa.

Ya bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da Janar Yakubu Gowon ya samar tare da ƙarfafa gwiwar gwamnatoci da su ci gaba da inganta NYSC don samun haɗin kan ƙasa.