✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na Yi Iya Kokarina A Matsayin Shugaban Najeriya —Buhari

Buhari ya bayyana a Amurka cewa ya iya wa Najeriya iya abin da zai iya a matsayin shugaban

Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya ce ya yi iya kokarinsa a matsayinsa na shugaban kasa don ciyar da Najeriya gaba.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da Babban Sakataren zauren samar da zaman lafiya na Abu Dhabi Forum, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah, tare da takwaransa na Amurka, Fasto Bob Roberts, suka ziyarce shi ranar Talata a birnin Washington DC na kasar Amurka.

“Najeriya babbar kasa ce da kuma yawan mutane da ke fuskantar kalubale iri-iri a wuarre daban-daban, amma na yi iya bakin kokarina tsawon shekaru bakwai da na shafe kan mulki,” in ji Buhari.

Cikin wata sanrwa da Kakakinsa Garba Shehu ya fitar, Buharin ya ce magance matsalolin da suka addabi matasa ne abin da gwamnatinsa ta sa gaba, domin cika alkawarinsa na samar da kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya.

Buhari ya ce akwai bukatar kyautata rayuwar matasa, don guje musu fadawa ayyukan masu tsattsauran ra’ayi, sannan ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da kai dauki kan matasa don su ne manyan gobe.

“Ayyukan da kuke yi na da matukar muhimmanci musamman ga matasa.

“Wannan babban yunkuri ne da zai taimaka wa al’ummar da za su rayu nan gaba cikin aminci.

“A namu bangaren za mu ci gaba da magance matsalolinmu musamman wadanda suka shafi matasa.

A nasa bangaren Sakataren gidauniyar Bin Bayyah ya ce sun kai ziyarar ce don gayyatar Buharin taron karrama shi da gidauniyar ta shirya, bisa nasarorin da ya samu a banagren inganta zaman lafiya da tsaro.