✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi bakin cikin tuhumar da ake yi wa Alkalin Alkalai- Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce, ya yi bakin cikin tuhumar da kotun da’ar ma’aikata CCT take yi wa alkalin alkalan Najeriya mai shari’a…

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce, ya yi bakin cikin tuhumar da kotun da’ar ma’aikata CCT take yi wa alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Walter Onnoghen akan laifin rashin bayyana kadarorinsa.

A ranar Litinin 14 ga Janairu 2019 ne, kotun ta yi zaman sauraran karar da aka shigar akan alkalin alkalan Najeriya.

Osinbajo ya bayyana wa kungiyar watsa labarai ta intanet (OPAN) hakan yau Laraba a Abuja, kuma yace shugaba Buhari bai da masaniya game da tuhumar da ake yi wa alkalin alkalan.