Ministar Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar Farouk ta ce ta yafe wa mutanen da suka zage ta game da zargin karkatar da kayan tallafin COVID-19.
Ministar ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tambayoyi daga manema labarai ranar Litinin a Gusau, Jihar Zamfara.
- ‘A kamo barayin kayan tallafin COVID-19 na Kaduna’
- An ci gaba da fasa rumbunan adana kayan abinci a Abuja
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Zamfara
- Mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara
“Ina da labarin yadda mutane suka rika zagi na da ma’aikatata game da kayan tallafin COVID-19 da Gwamnatin Tarayya ta bayar.
“Na sha fada cewa ni aikina nake yi kuma ina yin sa ne daidai karfina kuma yadda zan tallafa wa kowa dake kasar nan.
“Yanzu sun fahimci gaskiya cewa ba ni da laifi don haka ina fatan Ubangiji Ya yafe mana baki daya.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta samar da manyan tituna a kasar nan domin gano maboyar bata-gari, wanda hakan ne kadai zai saukaka aikin jami’an tsaro”, cewar ministar.
Kamfanin Dillacin Labarai na Kasa (NAN), ya rawaito cewa Sadiya ta kai ziyara ne ga Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, wanda a jawabinsa, ya roki Gwamnatin Tarayya a kan ta sake yin duba game da sha’anin tsaro a jihar ta Zamfara.