Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce ya yafe wa Shugaba Muhammadu Buhari duk wasu rashin daidai da ya aikata.
Ortom ya bayyana haka ne a yayin wata hira da ake yi da shi a shirin safiya na The Morning Show na tashar talabijin ta Arise a wannan Larabar.
- An maimaita fatali da yarjejeniyar sulhu a Sudan
- Rancen Paris Club: Gwamnati za ta dawo wa jihohi kudadensu
Gwamnan ya kasance yana sukar fadar shugaban kasar a kan yadda ya ce Gwamnatin Tarayyar na sukar gwamnatinsa a kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa.
A cewarsa, “Ya zama tilas na yafe wa Buhari, domin a matsayina na Kirista kuma kamar yadda ya tabbata a littafin addininmu, Ubangaji ba zai yafe maka ba idan ba ka yafe wa jama’a ba.”
A baya-bayan nan shugaban kasar ya nemi afuwa daga ’yan kasar da suke ganin mulkinsa ya kuntata musu.
Kazalika, Ortom ya kuma ya shawarci shugaban mai barin-gado da ya tsaya a kasar ya taimaka wa sabuwar gwamnati mai zuwa ta Bola Tinubu domin ciyar da kasar da ma jiharsa gaba, kamar yadda ya ce.