✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na tafi karuwanci Dubai amma na kare a Mali

Sun tashi zuwa yawon karuwancin a Dubai amma suka makale a Mali.

Wata matashiya mai shekara 21, Irhobisa Lawrence Orhumnzie, ta koka da yaudarar da magajiyar ta yi mata na kai ta karuwanci Dubai amma suka kare a kasar Mali.

Orhumnzie, ta yi wannan bayanin ne bayan hukumar IOC ta kwaso su zuwa Najeriya bayan sun makale a Mali sakamakon annobar COVID-19.

Orhumnzie wadda tana cikin mutum 109 da aka kawo Filin Jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas ta ce an tafi da ita yawon karuwancin ne tare da wasu ‘yan mata 24, da sunan za a kai su Dubai.

“Mun tashi daga Legas, muka ratsa Kwatano da Jamhuriyar Benin da Togo, daga nan muka shiga kasar Mali.

” Muna shiga Bamako, ‘yan sandan Mali suka damke mu, suka tambaye mu ko za mu koma Najeriya muka ce, eh.

“Daga nan suka kai mu ofishin jakadancin Najeriya da ke Mali amma ba a samu damar maido mu ba saboda COVID-19. Sai yanzu IOC ta taimaka muka dawo”, inji ta.