Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ya taɓa zama kurma ba tare da ya sani ba, har sai da aka masa gwaji.
Obasanjo ya bayyana haka ne, a Bauchi ranar Asabar lokacin da ya kaddamar da rabon na’urorin da ke taimaka wa kurame da jin magana sama da 10,000 a yankin Arewa maso Gabas.
- Shettima zai wakilci Najeriya a taron CHOGM na 2024
- Tsadar rayuwa: Mutanen da suka karɓi taliya sun fi shan wahala — Damagum
Rabon ya fara daga jiharsu Bauchi inda aka bai wa mutum 2,000 tallafin na’urar.
Obasanjo, ya ce mutane da yawa suna fama da cutar rashin jin sautin magana yadda ya kamata sun zama kurame ba tare da sun sani ba.
Tsohon shugaban, ya bayar da labarin yadda ya je kasar waje yin aiki amma daga bisani ya gano ba ya jin magana yadda ya dace.
Obasanjo ya ce daga bisani an duba shi sannan aka tabbatar masa da cewar jin maganarsa ya ragu da kashi 25 cikin 100.
“Bayan sakamakona ya fito, sai na nemi mutumin da ya duba babban jami’in tsarona a lokacin amma abin mamaki, shi ya fi ni kurmancewa don shi rashin jinsa ya fi karfin kashi 25.” In ji shi.
Ya ce, wannan ne dalilin da ya sa ya kafa gidauniyarsa ta Olusegun Obasanjo inda ake duba dubban ‘yan Nijeriya domin dakile rashin jin magana.
Ya godewa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed bisa kokarinsa na samar da ayyukan ci gaba a jihar.
Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed, ya yaba wa tsohon shugaban ƙasar, kan ayyukan alheri da yake yi wa Nijeriya.
Kazalika, Obasanjo ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu.
Obasanjo ya shaida wa Sarkin cewa, dole ne kowa ya tashi tsaye wajen tunkarar matsalar tsaro a kasar nan ta hanyar yin aiki tare da al’umma.