✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na so a ce ’yata ta kammala karatu kafin ta auri dan Buhari – Sarkin Bichi

Ya ce ya kan shiga tsaka mai wuya a duk lokacin da zai aurar da ’ya’yansa.

Mai Martaba Sarkin Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce ya so a ce ’yarsa, Zahra ta kammala karatunta kafin ta auri Yusuf, da ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Za dai a daura auren Zahra da Yusuf ne ranar Juma’a, 20 ga watan Agustan 2021 a Fadar Sarkin na Bichi bayan Sallar Juma’a.

To sai dai a cikin wata tattaunawarsa da Aminiya, Sarkin ya yi bayani a kan dangantakarsa da ’ya’yansa.

Ya ce ya kan shiga tsaka mai wuya a duk lokacin da zai aurar da ’ya’yansa saboda shakuwarsa da su.

“Ina da kusanci da ’ya’yana sosai, saboda aurar da Zahra ma ba karamin tsaka mai wuya ya saka ni ba, amma Alhamudillah.

“Karamar yarinya ce, shekararta 20 kacal, kuma tana shekarar karshe ne a jami’a inda take karantar Fasahar Zane-zanen gine-gine (Architecture).

“Na so a ce ta samu ta kammala karatunta a jami’a, sannan ta dan zauna da mu ko da kadan ne, amma ba haka Allah ya tsara ba, kuma ba zamu iya canza ikonSa ba, sai dai kawai mu yi musu fatan alheri,” inji shi.

Watakila, Sarkin ya dada shiga damuwar ne kasancewar a farkon shekarar nan ma ya aurar da wata diyar tasa.

To amma fitaccen dan kasuwar kuma basaraken, wanda kuma shine Shugaban kamfanin sadarwa na 9mobile da ma wasu kamfanoni da dama ya ce ya sami natsuwa ne daga wani Hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa, “Duk wanda Allah ya ba ’ya’ya mata har guda uku, ya tarbiyyantar da su har ya aurar da su, zai shiga Aljannah.”

“Wannan shi ne fatana, cewa ta sanadiyyarsu, Allah zai bani Aljannah,” inji shi.

Sarkin, wanda nan da ’yan kwanaki za a yi bikin ba shi sandar mulki ya kuma yi bayani a kan batututwa da dama, ciki har da alakarsa da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.