Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan rashin samun damar ziyartar Jihar Zamfara kamar yadda ya shirya zuwa a ranar Alhamis, a sakamakon rashin kyan yanayin hazo a ranar.
Mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Buhari ya bayyana damuwarsa matuka cikin wani bidiyo da ya aike wa al’ummar Zamfara, a yammacin ranar Alhamis.
“Na damu sosai sabodab ban samu kasancewa da ku ba kamar yadda na tsara.
“Na gama halartar taron kamfanin BUA a Sakkwato kuma ina shirin zuwa haduwa da ku. Amma sai aka sanar da ni cewa ba zan samu damar zuwa Zamfara ba saboda jirgi ba zai iya tashi daga Sakkwato zuwa Gusau ba, saboda yanayin da aka tashi da shi.
“Na san yadda kuke ji a ranku game da wannan labari, amma ina da yakinin za ku fahimce ni kuma Allah Shi ne shaida.
“Ina yi wa Gwamna Bello Matawalle, shi da mukarrabansa jaje kan yadda suka yi ta fadi tashin ganin wannan ziyara ta kasance, amma abubuwa ba su tafi yadda ake so ba.
“Ina fatan samun wani lokacin da ya fi dacewa da zan kawo muku ziyara,” cewar Buhari.
Shugaba Buhari ya jadadda aniyarsa ta ganin gwamnatinsa ta kakkabe ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara za su ci gaba da aiki tare wajen tabbatar da samuwar zaman lafiya da tsaro a jihar.
“Ina ba wa jami’an tsaro umarnin su ci gaba da bankado duk inda wata maboyar ’yan ta’adda take sannan su murkushe su baki daya a jihar.
“Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Zamfara na aiki tare a kodayaushe don ganin an samar da zaman lafiya a dukkanin sassan jihar.
“Allah Ya albarkaci al’ummar Zamfara.”