Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya san yadda zai farfado da tattalin arzikin Najeriya fiye da sauran abokan karawarsa a zaben da ke tafe.
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, a lokacin yakin neman zabensa.
- Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da karancin abinci a duniya – IMF
- IMF ya shawarci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi
Tinubu ya ce, “Na san yadda zan yi. Na san yadda zan yi fiye da sauran ‘yan takara. Ni mutum ne da ya san hanya. Mutum ne da ya san yadda zai samar wa kasa kudi. Mutumin da yake cika alkawari,” a cewarsa.
Ya ce mutane da yawa sun nuna damuwa kan yadda ya yi korafi game da sabon tsarin canjin kudi, inda ya ce ya zuwa yanzu za a bar komai a hannun kotun koli har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
Tinubu, akwai jihohi da dama da suke da albarkatun kasa, zai taimaka musu wajen gano su tare da cin moriyarsu.
Kazalika, ya ce zai farfado da kamfanin sarrafa man fetur na Ajaokuta da fadada kogin Neja sannan zai tada kamfononi da suka durkushe tare da inganta harkar noma da samar da ayyukan yi.
A nasa jawabin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai tarin basira.
Bello ya kara da cewar idan Tinubu ya dare karagar mulkin Najeriya, “Zai farfado da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta. Matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan ma zai magance ta,” in ji shi.