’Yan sanda a Jihar Kano sun kubutar da wani matashi mai suna Abba Ahmed daga yunkurinsa na kashe kansa bayan an kasa shi a neman auren diyar Shugaban Kasa, Hanan Muhammadu Buhari.
Matashin mai kimanin shekaru 22 wanda dalibi ne a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, a kwanakin baya cikin wani bidiyo da ya karade gari ya yi barazanar kashe kansa muddin bai samu auren Hanan ba.
Wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ba ta ce da jin haka ne Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa, Frank Mba umarci reshenta na Kano ya gayyaci Abba domin a yi wa tufkar hanci.
Majiyar ta ci gaba da cewa Frank Mba ya kuma jawo hankalin matashin kan ya fuskanci abubuwa masu muhimmanci a rayuwarsa kada ya hallaka kansa kamar yadda wasu suke kokarin tunzura shi a kafafen sada zumunta.
- An kama shi yana wa karamar yarinya fyade a cikin masallaci
- An daura auren diyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Bayan Kwamishinan ’Yan Sandan Kano CP Habu Sani shi ma ya ja hankalin matashin ne jikinsa ya yi sanyi ya kuma yi nadama har ma ya yanke shawarar shiga aikin dan sanda.
Abba mai sana’ar sayar da tufafi a kasuwar Kantin Kwari ya ce yadda Frank Mba da kwamishinan ’Yan Sandan Kano suka ba shi shawara shi ne ya burge shi har suka sa mishi sha’awar aikin nasu.
Ya ce, “Na hakura da batun kashe kaina kamar yadda na kuduri aniya tun da farko, zan tsaya in jira matata wacce take daidai da ni har na cimma sauran kudirorin rayuwata.
“Ina son Hanan ne saboda tana da kyau; tana burge ni saboda gaskiyar mahaifinta (Buhari).
“Na yi ta kokarin sanar da ita ta kafafen zumunta, amma ba na tunanin ta ga sakon. Na sha aike wa da mahaifinta ma da sako ta irin wadannan shafukan, ba na tunanin shi ma ya karanta gaskiya”, inji shi.
Tuni dai Abba ya kuduri aniyar fara sabuwar rayuwa tare da fatan samun matar da za ta zama daidai da shi.