Daya daga cikin shugabannin’yan Shi’a na yankin Birnin Tarayya Abuja wanda kuma shi ne wakilin Sheikh Ibrahim Zakzaky a yankin Gwagwalada, Malam Abubakar Zaki ya bayyana yadda ya rasa ’ya’yansa mata hudu a yayin arangamar sojoji da mabiya Shi’a a garin Zariya.
Malam Abubakar Zaki, wanda ya rasa suruki a artabun na Zariya, ya ce ’ya’yansa da ya rasa sun hada da Nusaiba Abubakar wadda ya ce daliba ce a Jami’ar Abuja, sai kanwarta Fatima Abubakar da ke shirin zuwa Kwalejin Ilimi ta Abuja da ke Zuba, sai kuma babbar ’yarsa A’isha Abubakar wadda ta rasu tare da ’yarta ta goye mai suna Fatima Batula da kuma mijinta Buhari Bello Jega wani dan jarida mazaunin Abuja.
Ya ce wani dan uwa da ya je taron shi kadai daga garin Gwagwalada mai suna Salisu Idris sun daina jin duriyarsa bayan aukuwar lamarin, “Bayanai sun ce an yi masa gani na karshe ne a wani waje da aka bude wuta a kan mutane a Zariya,” inji shi.
Ya ce amma kanensa mai suna Abdullahi Muhammad da ya je tare da ’ya’yan nasa ya kubuta kuma ya dawo gida.
Ya ce, “A’isha Abubakar Zaki ’yar wana ne, wana ya haife ta, amma ni na rike ta bayan rasuwarsa, sai kuma ’yata Nusaiba Abubakar, sai Fatima Abubakar, sai kuma jikata ’yar ita A’isha mai suna Fatima Batula, sai kuma surkina Buhari Bello Jega mijin A’isha ’yar tawa shi dan jarida ne, ya rasu tare da matarsa da kuma ’yarsu ta goye mai shekara daya da wata shida.”
Malam Abubakar Zaki ya ce Nusaiba da Fatima ba su yi aure ba tukuna, “Nusaiba tana shekara ta biyu a Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, ita kuma Fatima ta samu gurbin shiga Kwalejin Ilimi ta Abuja da ke Zuba. Kuma sun bar gidana da ke Gwagwalada a ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na yamma suka nufi Zariya, inda suka isa Zariya cikin dare,” inji shi.
Ya ce a lokacin da suka tafi Zariya ba ya da labarin an fara artabun, kuma sun je ne domin halartar taron sauya tuta. “Kamar yadda aka saba a farkon watan jiya ake kafata tutar bakin cikin rashin (Imam) Hussaini a duk shekara, idan aka shiga watan Maulidi kuma, sai Malam ya cire ta ya sauya ta da ta farin cikin haihuwar Manzon Allah (SAW). Akan yi haka ne da misalin karfe 4:00 zuwa 5:00 na maraice, sannan bayan Sallar Magariba da Isha’i, sai Malam ya yi jawabai har zuwa wani lokaci,” inji shi.
Shugaban ya ce wayarsa ta karshe da ya yi da ’ya’yansa ita ce wadda ’yarsa Nusaiba ta yi masa a ranar Lahadi da misalin karfe 6:00 na safe daga Unguwar Gellesu, gidan Sheikh Zakzaky, ya ce a yayin wayar ta shaida masa cewa “Abba ka yafe mana zai yi wuya mu sake haduwa a yanzu, an harbe ni a ciki, ita kuma A’isha an harbe ta a kai. Sannan ta sanar da ni Buhari mijin A’isha shi aka fara harba, ita kuwa Fatima wadda tana tare da su ta kira kanena Abdullahi wanda ya tsira daga al’amarin, ta sanar da shi ga shi fa ana harbe jama’a, ya tambaye ta kina ina, ta sanar da shi, sai ya shawarce ta, ta kwanta kada ta motsa kuma ta daina magana, shi ma yana ta wajen, to, watakila daga baya ne suka karaso kanta suka harbe ta, daga nan dai magana da ita ta tsaya,” inji shi.
Buhari Bello a karshen rayuwarsa
Jaridar NewsRescui da ake bugawa a Intanet ta ruwaito abubuwan da Buhari Bello ya yi a karshen rayuwarsa kamar haka: “A ranar 12 ga Disamba da yamma Buhari ya nufi Zariya daga Abuja. Sheikh Zakzaky ne ya aiko da sako cewa sojoji sun fusata suna kokarin hana su gudanar da harkokin addininsu, sun fito da karfinsu don haka mabiya su zo su kare cibiyarsu ta Musulunci da ’yancinsu na yin addini.
Abokin Buharin ya ce a cikin rukunin tattaunawarsu, ya yi kokarin ya lallashe shi cewa kada ya tafi (Zariya) tunda labari ya watsu cewa sojoji suna kashe Musulmi a can.
Buhari Bello ya rubuta a shafinsa na facebook kan yadda sojoji suka auka musu a Husaniyyah a daukacin dare zuwa wayewar gari.
Ya bayyana yadda sojojin da suka kafa tunga cikin shirin fada a wajen cibiyar suka rika bude wuta ga duk wani abu mai rai ko mai motsi da ke cikin cibiyar da yadda suke sanya bam ga ginin.
Da misalin karfe 2:37 na dare ya rubuta cewa: “Abin kunya da rikicewa a bangaren sojin Najeriya a daidai lokacin da suke fuskantar babban abin kunya a rayuwarsu… sun karkashe tare da raunata ’yan uwa maza da mata da yawa, amma duk da haka mun ci gaba da zama lafiya. Sun sa rai za mu yi fito-na-fito, amma abin da kawai suke ji shi ne, “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!” Ya Mahdi! Ya Mahadi!! Ya Mahadi!!! Da suke fitowa daga ’yan uwa maza da mata da yara… abin kunya game da fitowar yaran Yahudawa… a daidai lokacin da kunya da rashin nasara ke zuwa musu… duk da karo sojoji da makamai da karfin harbi, karfin hali da jajircewar ’yan uwa maza da mata ya fara kankama…ba za ku sanya mu yin abin da kuke so ba, mu Musulmi ne… masoya Muhammad da iyalan Muhammad… muna da ka’idoji na fafatawa… ba za a fusata mu mu yi abin da kuke so ba… Ku karanta Musulunci… addini ne na kare kai ba na takala ba… kuma akwai matakai da hanyoyin bi kafin a fara Jihadi… don haka ba za ku sa mu yi abin da kuke so bisa jahilci da yaudararku ba #mamayehusainiyyabakiyatullah.”
Da karfe 3:25 na dare sai Buhari ya sake cewa: “Yanzun nan sojin Najeriya suka samu lambar zinare na tsoro ta hanyar sanya bam a gaban ginin Husainiyyah Bakiyatullah…wani kara mai karfi ya yi rugu-rugu da gaban ginin Husainiyyah Bakiyatullah, kamar yadda labari ke iso mana yanzu… mene ne manufar wannan? Shin Husainiyyah ta koma sabon dajin Sambisa ne?”
A karshe sai Buhari Bello ya rubuta cewa yana fata Allah Ya gafarta masa, haka duk wanda ya yi wa laifi, “Ana iya kashe ni a kowane lokaci daga yanzu, kuma a shirye nake in hadu da Ubangijina.”
Da misalin karfe 4:24, Buhari ya rubuta sakonsa na karshe kafin ya rasu a wannan ne sako na karshe ya ce: “Kaito, batirina na neman macewa kuma wannan na iya zama sakon da zan rubuta na karshe…asuba ta yi ana ta kiran Sallah… koma wane hali ne ku gafarta mana, tara muke, amma muna kokari ne mu ga wace gudunmawa za mu bayar ta yadda za mu samu uzuri a gaban Allah lokacin da ya tambaye mu game da me muka yi wa Musulunci… za mu iya cewa Ya Ubangiji mun yi iyakar kokarinmu kuma a kokarin yin haka ne muka yi shahada.”
Wakilin Zakzaky na Suleja Malam Hasan Adamu ya ce sun samu tabbacin rasa mutum uku a cikin al’amarin daga cikin mutum shida da ba su dawo ba, kuma aka daina jin duriyarsu. Ya ce mammatan su ne: Malam Yawale wani magidanci da Junaidu Abubakar da Malam Mudassir Bala wani likita.
Amma wani dan fafutikar kare hakkin jama’a na kungiyar mai suna Muhammad S. Muhammad ya kubuta.
Zakzaky ya sake rasa ’ya’ya maza uku
da namiji daya da ya saura a cikin ’ya’yan Sheikh Ibrahim Zakzaky, Muhammad Ibraheem ya ce sojoji sun kashe uku daga cikin sauran ’ya’yan malamin maza a harin na makon jiya.
Muhammad Ibraheem ya ce ’yan uwansa maza uku da suka hada da – Hammad mai shekara 17 da Ali mai shekara 15 da kuma Humaid mai shekara 13 – duk an harbe su a gaban mahaifinsu a lokacin farmakin da aka kai gidansu a Zariya a ranar Lahadin makon jiya.
A wata sanarwa da ya fitar, Muhammad ya ce daga cikin ’yan uwansa takwas yanzu saura su uku ke raye wato shi da Nusaiba da Suhaila, yayin da saura shida sojoji suka kashe su a bara da bana.
Ya ce Suhaila ma ta tsira ne tare da rauni a fuskarta. Kuma wata yayar Zakzaky mai suna Fatima Yakub tana cikin wadanda aka kashe a harin, yayin da malamin da matarsa suka tsira da harbin bindiga.
Muhammad Zakzaky ya ce, za su ci gaba da zanga-zanga don neman a ba su damar binne matattunsu yadda ya kamata tare da ganawa da wadanda suka samu rauni da kuma nema wa jagoransu kuma babansa lafiya. Kuma ya ce za su ci gaba da neman ganin an yi adalci ga ’yan uwansa shida matukar yana numfashi.