✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na ki karbar aikin gwamnati saboda sana’ar fim – Ali Nuhu

Tauraro a masana’artar Kannywood Ali Nuhu ya bayyana yadda mahaifinsa ya taba sama masa aikin gwamnati amma ya ki karba saboda ya fi son sana’arsa…

Tauraro a masana’artar Kannywood Ali Nuhu ya bayyana yadda mahaifinsa ya taba sama masa aikin gwamnati amma ya ki karba saboda ya fi son sana’arsa ta wasan fim.

Ali Nuhu ya ce bayan ya kammala karatun digirinsa na farko, ya yi bautar kasa a garin Ibadan, har ya fara sana’ar fim a Kano, sai mahaifin nasa ya samar masa aikin gwamnati da ya ki karba.

“A lokacin da na dawo Kano ina da abokai biyu, Rabiu Ibrahim da Hafizu Bello suna so su shirya wani fim na kansu kowannensu.

“Sai suka shigar da ni ciki, suka bukaci na ja ragamar aikin fim din.

“A lokacin ne mahaifina ya samarmin aikin gwamnati, sai na ce masa a’a.

“Domin kudin da zan samu a fin din ya fi abin da za a rika biya na a wata, don haka na ce ni fim zan yi, ba aikin gwamnati ba.

“Lamarin ya zama gagarumi domin har sai da mahaifiyata ta shigo ciki ta yi ta ba wa mahaifina hakuri, har ya hakura, to haka abin yake”, inji Ali Nuhu.

Lokacin da Ali Nuhu ya karbi lambar karramawa a Indiya
Lokacin da Ali Nuhu da ya karbi lambar karramawa a Indiya

Fitaccen jarumin na Kannywood ya shaida haka ne a wata hira da wani kamfanin samar wa matasa aikin yi tare da ba su shawarwari ya yi da shi ta kafar sadarwar zamani na bidiyo.

Kamfanin ya yi hirar ne da Ali Nuhu domin ya ba wa matasa shawarwari tare da kwarin gwiwa a kan al’amuran da suke so su cimma a rayuwa.

Jarumi Ali Nuhu ya kuma bayyana irin kwazo da jajrcewa da ya yi a lokacin da yake kokarin cimma burinsa na zama dan wasan kwaikwayo.