Wani matashi da ake zargi da kisan dan acaba a Jihar Ogun ya ce ya kashe shi ne saboda ya sami kudin sayen data a wayarshi don yin damfara a intanet.
Dubun matashin mai suna Samson Odunayo, mai kimanin shekara 18, ta cika ne ranar Litinin bayan ya daddatsa dan acabar mai suna Bashiru Umaru sannan ya gudu da babur dinsa.
- Matsalar tsaro raguwa take ba karuwa ba a Najeriya – Buhari
- Najeriya A Yau: Yadda Aka Kashe Mutum 65 A Goronyo
An dai kama shi ne tare da sauran abokansa mutum biyu; Sodiq Awokoya da kuma Jimoh Rilwan ranar Juma’a, takwas ga watan Oktoban 2021 a yankin Ogere na Jihar, inda aka yi bajekolinsu a hedkwatar ’yan sandan Jihar da ke Abeokuta, babban birnin Jihar.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ce matasan sun shiga hannu ne a daidai lokacin da suke kokarin sayar da babur din.
Samson dai, wanda ya shaida wa ’yan jarida cewa shi dan damfara ne ta intanet (wato Yahoo), ya kuma ce ya aikata laifin ne saboda yana tsananin bukatar kudin sayen data a lokacin.
Ya ce, “Sadik ne ya koya min ayyukan laifi, wannan kuma shi ne karo na biyu da muke aikata irin wannan kafin a kama mu.
“Amma a na farkon da muka yi, ba mu kashe kowa ba, kawai dai mun karbi N3,500 daga hannunsa.
“Na yanke shawarar aikata laifin ne saboda in sami kudin da zan sayi data don in yi damfara ta intanet. Ban taba kashe kowa ba kafin wannan karon,” inji shi.