Akwai bukatar mahukunta su kara himma sosai wajen samar da hanyoyin rage radadin bakin talaucin da al’ummar kasar nan suke fama da shi a halin yanzu domin kuwa talaucin kullum sai karuwa yake yi ta yadda yanzu kusan kowa ta kansa yake yi domin abin da yake samu ba ya isarsa balle ya rage ya taimaka wa wani, wato an shiga lokacin nan da ake cewa ‘nafsi-nafsi’ ke nan.
Masu hali da dama wadanda suka fi karfin abin da za su ci kuma suke taimaka wa ’yan uwansu, yanzu su ma ta kansu suke yi, domin samunsu ya yi kasa sosai, bai ishe su ba balle su taimaka wa wadansu.
Wadanda suke da sauran karfi kuma har suke iya ci gaba da taimakawa, nauyin na neman dankare su har su kasa ci gaba da taimakon da suke yi, saboda masu bukata a gare su sun yi yawa kuma kullum karuwa suke yi ba raguwa ba.
Ko a ranar Litinin da ta gabata gidan Rediyon BBC ya yi hira da wani bawan Allah a Jihar Katsina da ya canja sunan dansa mai shekara hudu daga Muhammadu Buhari zuwa Sulaiman. Ya ce ya yi haka ne saboda nuna damuwarsa dangane da matsanancin halin da ya shiga a zamanin mulkin Shugaba Buhari.
Wannan bawan Allah ya bayyana cewa shi dan Jam’iyyar APC ce gaba da baya kuma mai matukar kaunar Shugaba Buhari, amma sai ya kasance a zamanin mulkin Shugaba Buhari ne ya fada cikin talaucin da bai taba zato ba.
Ya ce shi dan kasuwa ne da yake da rufin asiri daidai gwargwado, har ta kai ga saboda wadata yana iya canja mota kamar yadda yake iya canja riga kuma yana da sauran kadarori, sai ya kasance an kama dan uwansa an yi garkuwa da shi, sai da ya sayar da wasu kadarorinsu ya samu ya kubutar da shi, haka dai matsaloli suka yi ta fada masa har sai da ya kai a halin yanzu komai nasa ya kare, ko taya bai mallaka ba.
Ya ce ganin yadda duniya ta yi masa daurin minti ne, gaba dauri, baya dauri, shi ya sanya ya yanke shawarar canja wa dansa suna daga Muhammadu Buhari zuwa Sulaiman domin kuwa bai ji dadin mulkin Shugaba Buhari ba.
Mutane irin wadannan suna da yawa a halin yanzu, wadanda attajirai ne amma yanzu sun zama abin tausayi. Misali, akwai wani bawan Allah da ya ce wata rana suna tafiya a kan hanyarsu ta zuwa gida su hudu, ganin yadda suke tafiya a kasa sai ya dubi sauran ya ce ‘a da fa dukkanmu muna da motocinmu na shiga amma yanzu ga shi duk mun rasa motocin mun koma muna tafiya a kasa.’
Wadansu mutanen sun yi wa kasa aiki ne sun gama amma ba a biya su hakkokinsu ba, wadanda kuma ake biya ana ba su hakkokin nasu ne gutsul-gutsul ta yadda ba za su yi musu amfani sosai ba.
Lallai ya kamata shugabanni su himmantu wajen samar da hanyoyin inganta arzikin al’ummominsu, domin kuwa ana gane nasarar da shugaba ya samu ne ta la’akari da yawan mutanen da suka azurta a zamaninsa, idan kuwa har ya kasance maimakon a samu karuwar ma’azurta sai karin matalauta ake samu to lallai akwai matsala, domin wannan ya nuna cewa ana kara nakasa na kasa ke nan maimakon a agaza masa ya mike sosai.
Wajibi ne hukumomi su sake nazarin matakan da suke dauka da nufin sassauta wadanda suka yi tsauri da yawa, yadda mutane za su samu damar yin walwala su samu karuwar arziki da kwanciyar hankali.
Dole ne a kara himma wajen inganta tsaro, domin idan babu tsaro mutane za su zauna a cikin tsoro, ’yan ta’adda su yi ta cin karensu babu babbaka, su yi ta raunana mutane raunana saboda zaluntarsu da ake yi a kullum.
Yanzu haka gwamnati sai kokari take yi ta dadada wa manoma saboda a mayar da hankalin mutane zuwa gona, amma matsalar tsaro ta takura wa manoman, domin wadansu sun yi kokari sun yi noman, amma sun kasa zuwa gonakin nasu su kwaso amfanin gonar saboda gudun fadawa hannun masu garkuwa da mutane.
Haka kuma hakkin gwamnati ne ta taimaka wa talakawanta wajen samun lafiya ta hanyar inganta asibitocinta yadda talaka zai iya samun magani a kowane lokaci da sauki, maimakon ya zauna a gida ciwo na cinsa babu yadda zai yi saboda talauci ya dabaibaye shi.
Irin abin da ya faru ke nan da iyayen yarinyar nan ta Jihar Zamfara da ta zuba wa kanta kananzir ta banka wa kanta wuta saboda an hana ta wanda take so ta aura, iyayenta sun ce sun kasa kai ta asibiti nan da nan ne saboda a lokacin da abin ya faru Naira 700 kacal suke da shi a duk gidan nasu. Shi ya sanya suka kwashe ta zuwa wurin mai maganin gargajiya, domin ba su da kudin zuwa asibiti.
Haka nan iyaye suke ta fama da matsaloli a halin yanzu, ta yadda idan yaro ba ya da lafiya shi da kansa zai rika yi wa iyayensa kuka yana cewa ‘Don Allah baba a kai ni asibiti,’ amma saboda talauci sai dai su zura masa ido su yi ta lallashinsa.
Saboda haka don Allah gwamnati ta rika sauraron talakawanta, idan sun koka a saurari kukan nasu, kada ta rika sauraron maganar fadawa kawai wadanda miyarsu kadai suke kokarin gyarawa.
Domin idan tsanani ya yi yawa miyagun laifuffuka karuwa suke yi, saboda mutumin kirki wahala tana sanya shi ya zama mutumin banza.