✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na kai ’yan kwallo da yawa Golden Eaglets – danjuma Manaja

Aminiya ta samu tattaunawa da danjuma Hussaini wanda aka fi sani da Manaja, wanda ejan ne na ’yan wasan kwallon kafa da ya yi fice…

Aminiya ta samu tattaunawa da danjuma Hussaini wanda aka fi sani da Manaja, wanda ejan ne na ’yan wasan kwallon kafa da ya yi fice wurin zakulo ’yan kwallo musamman ’yan kasa da shekara 17, yana yi musu hanyar buga wasa a kungiyar kwallon kafa ’yan kasa da shekara 17 wato Golden Eaglets. Daga cikin wadanda ya yi musu ejan akwai dan wasan kungiyar Super Eagles, Simon Moses da Crisantus Macauley da Simon Zenke da Lukuman Abdulkareem da sauransu:

Ka gabatar da kanka da kuma abin da ya ja ra’ayinka a harkar horar da ’yan kwallon kafa?
Sunana danjuma Hussaini da aka fi sani da Manaja ina zaune a Hayin Banki, Kaduna, kuma abin da ya ja hankalina shi ne son wasan kwallon kafa da kuma duba cancantar ’yan wasan.  
An ce kana taimaka wa ’yan wasa ka dago su domin buga wasa a kungiyar Golden Eaglets mene ne gaskiyar wannan batu?
Kamar yadda na ce cancanta, ina duba wadanda suka cancanta ne domin in kai su, saboda ina jin takaicin ganin wadanda ba su cancanta ba a ce su ne suke zuwa kungiyar. Saboda haka ne na ga ya kamata in bi domin in duba wadanda suka cancanta sai in kai su.
Zuwa yanzu kamar ’yan kwallo nawa ne ka taimaka musu?
Suna da yawa sosai, akwai kamar su Simon Zenke da ake ce wa Terwase da Crisantus Macauley da Moses Simon da aka fi sani da Ajala da Michael Eneramo da Promise Onu da aka fi sani da Smally da Joshua Obaje da Abubakar Yahaya da sauransu wadanda a gaskiya ba su iya lissafuwa.
To kana taimaka musu zuwa Golden Eaglets ne kawai ko har da bugawa a kungiyoyin da ke rukunin Firimiya na Najeriya?
Manaja: Babu wanda bai kamawa, ina taimaka musu buga wasanni na gida da Golden Eaglets saboda dangantakar da nake ita da Manu Garba tun yana mataimakin Koci Izilia. A lokacin ne na kai Simon Zenke a nan filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, kuma lokacin da yake mataimakin Koci Yemi Tella  na kai masa Crisantus Macauley da Lukuman Abdulkareem a filin wasa na Liberty da ke Ibadan, sannan lokacin da ya zama babban mai horarwa na ’yan kasa da shekara 15 na tallafa a kan wadansu kamar su Musa Yahaya da Moses Simon da ke buga wa Super Eagels a yanzu, kuma har yanzu ina ci gaba da taimakawa.  
To a nan gida Najeriya kamar wadanne kungiyoyi kake taimakawa ’yan wasa su je?
A takaice na taimaka wa ’yan wasa da dama a Kaduna, ba a fadata ba, mutane suna cewa zai yi wuya a samu wanda ya taimaka wa yara a wasannin rukunin na Najeriya irina. Daga cikin wadanda na taimaka musu akwai wadanda sun daina buga kwallo, akwai wadanda suke ci gaba da bugawa, wadansu kuma sun fara a nan Najeriya, sun fita suna bugawa a kasasen waje. Kamar Promise Uno wanda ya taba zama wanda ya fi iya tsaron baya a Rukunin Firimiya na Najeriya wanda na dauko shi daga Pepsi Academy na kai shi gasar cin Kofin Gwamna a Jihar a Neja daga nan na kai shi Lafiya Scorpion daga nan na kai shi Jigawa Golden Stars sannan na kai shi Wikki Tourist da ke Bauchi har ya zama mai tsaron baya mafi kyau, aka kira shi domin ya buga wa Super Eagles. Sannan Joshua Obaje shi ma na fara da Jigawa Golden Stars daga baya ya koma Afirka ta Kudu da wasu kasashen Larabawa kafin ya dawo gida inda yake buga wa Plateu United. Akwai Abubakar Yahaya na fara daga Jigawa, akwai wadanda na kai su Sharks da kef Fatakwal irin su dan kasim da sauran wadanda na manta su.
Ta yaya kake zakulo ’yan kwallon?
Yadda nake gani shi ne kamar yadda na fada a farko, wato ina duba cancanta ne kuma ana ce min mai dubo ’yan wasa (scouter) nakan bi gari-gari, unguwanni-unguwanni in duba ’yan wasa ba sai ’yan unguwarmu ba. Ko daga wane gari kake in dai ka cancanta zan dauko ka in kawo ka, kuma na yi Manaja a kananan kungiyoyin kwallo, to, duk a nan ne nake dubawa sai in dauko wanda ya cancanta.
Har yanzu kana manajan wata kungiya ce ko ka kafa taka ce?
Har yanzu ina Manajan wasu kungiyoyin kamar su Unity FC da ke Filin Minista a NDA Bus Stop, Kaduna. Kuma ina da tawa kungiyar karama mai suna Alheri Stars FC, na kafa kungiyar ce domin in taimaka wa yaran unguwarmu da kewaye da ba su da damar zuwa wani wuri, sai na kafa kungiyar horar da su in zabi wanda ya cancanta in kai shi gaba.
Mene ne burinka da wannan gungiya?
Burina shi ne ina so kungiyar ta zama matakala ga ’yan wasa kanana, daga nan ne zan dubi wanda ya cancanta sai in tura shi gaba. Sannan duk yaron da ya zo ya samu horo za mu iya tura shi wata kungiya da ke nan Najeriya ko mu hada shi da wani babban manaja da ke da halin fitar da shi waje. kungiyar Alheri Stars FC ba ta unguwa ba ce, kowa zai iya zuwa domin akwai yaran Kaduna, akwai na Abuja, akwai dan Lagos yanzu haka a kungiyar.
Mene ne bambancin yanayin kwallon kafa na nan Najeriya da na kasashen waje?
Akwai bambance-bambance da dama, domin akwai kayan aiki da suke da shi wadanda ba mu da su, akwai abubuwa da suke karanta wadanda ba mu kawo wurin ba a gaskiya. Akawai mu da yara masu baiwa in baicin haka da ba za mu iya buga kwallo da su ba, kuma su suna duba wanda ya cancanta ne, mu kuma muna sanya siyasa a harkar, siyasa ta ’yan siyasa da siyasar masu horarwa da siyasa ta manajoji. Domin dan siyasa zai iya zuwa ya ce sai an sa wani yaronsa koda bai cancanta ba, kuma wasu manajojin, wadanda suke da kudi suna zuwa su ba da kudi su ce a dauki yaronsu koda bai cancanta ba mu wanda mu ba za mu iya ba da wannan kudi ba. Sannan su ma alkalan wasa ba sa hura gaskiya sai ’yan kadan. Domin za ka ga idan aka zo gidan wata kungiya wasa ba za a ci ta ba, domin za ta saye ’yan wasa da jami’an tsaro da wakilin Hukumar NFF ta ci wasa. To ka ga wanda yake sayen wasa ba zai iya sanin dan kwallo mai kyau ba. Da a ce ba a amfani da kudi domin sayen wasa, dole a nemi kwararrun ’yan wasa da suka cancanta domin su ci wasa saboda kwarewarsu.
Aminiya: Wadanda ka taimaka musu suna tunawa da kai bayan sun samu alheri ko sai labari?
To an ce gaskiya daci gare ta, amma gaskiyar magana ba sa yi, kuma gara in fadi gaskiya kada na yi wa kaina dungu. Ba su yin min komai kan irin taimakon da na yi musu. Ya kamata su dubi yanayina su taimaka min. Domin abin da nake lura da shi shi ne, ba wai ka ba yaro kifi ba, gara ka nuna masa yadda ake kamun kifin domin ya ciyar da kansa gobe. Shi ya sa nake daukarsu in kai su inda za su samu ci gaba. Kodayake mutane suna cewa halin dan kwallo ke nan, to ni dai har yanzu ban samu wanda ya zo ya taimaka min ba, amma dai ina sa ran wadansu mutum biyu da idan Allah Ya sa sun samu nasara ina da tabbacin za su taimaka min, amma dai a yanzu babu wanda ya zo ya share min hawaye, na dai yi musu sun samu kawai.
Ko hakan zai sa ka daina taimakon wadansu?
To a gaskiya ka sosa min inda ke min kaikayi, a da na so in bari, saboda kamar yadda dankwairo yake cewa sana’ar da babu riba, rike ta ba siriyos ne ba. To ba wai ribar ba ce babu akwai abin da ake ce wa lokaci, domin ana cewa wata rana akwai wanda zai zo daga inda ba ka yi zato ba, amma dai har yanzu ban ga wannan ba, sai dai ina fata Allah Ya kawo min shi. Sai dai kuma kananna biyu din da na fada, kuma gaskiya hakan bai karfafa min gwiwa yadda ya kamata. Amma duk da haka zan ci gaba, domin yanzu haka ma akwai wadansu da zan fitar da su, inda zan iya da kaina zan kai su, idan ya yi nisa sai in hada su da manyan ejan da zasu fitar da su waje.
Mece ce shawararka ga gwanmati game da harkar kwallon kafa?
Da gwamnati za ta gane, babu abin da ya kamata ta taimaka masa kamar wasan kwallon kafa, misali kamar yadda Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ke da burin samar da aikin yi ga matasa, da zan ba shi shawara, sai in ce ya taimaka wa kwallon kafa, za ka ji ana cewa ’yan shara ko ’yan daba da wuya ka ga dan kwallon yana wannan ta’addanci domin yana tunanin nan gaba zai zama wani abu ta hanyar kwallo. kuma tunaninsa zai buga kwallo da kafarsa ce, don haka ba zai bari a karya masa kafar da zai nemi abinci da ita ba. Don haka ya kamata a tallafa wa harkar kwallo sosai domin a magance ta’addanci. Sannan ba gwamnati kawai ba, har da masu kudi ya kamata su shigo harkar kwallo sosai.
A  karshe wane sako kake da shi ga magoya bayan kwallon kafa?
Manaja: Masu sha’awar kwallon kafa ya kamata su taimaka wa ’yan kwallo da ita kanta kwallon, su taimaka musu da kudi da shawarwari, sannan iyayen ’yan wasa suke fada musu su rika taimaka wa wadanda suka taimake su. Domin an ce yaba kyauta tukuici, sannan gwmnati ta kafa wata hukuma da za ta rika zama da masu kungiyoyin kwkllon kafa saboda lura da harkar sosai ba wai hukumar je-ka-na-yi ba. Domin kwallon kafa na rage shaye-shaye da ta’addanci, domin babu dan kwallon da yake ta’addanci saboda tunaninsa da burinsa nan gaba zai samu kudi a harkar. Su kuma ’yan kwallo shawarata gare su ita ce su rike amanar masu horar da su da manajojinsu da duk wanda ya tallafa musu, su tabbatar sun taimaka musu. Kuma kungiyoyin kwallon kafa su rike amanar yaran da aka ba su, kuma su daina yaudara.