Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan harin da ’yan bindiga suka kai kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata, inda ya ce ya damu matuka da harin, wanda shi ne irinsa na biyu a baya-bayan nan da ’yan bindigar suka kai.
- Harin jirgin kasa a Kaduna: Dokta Chinelo, ina kike?
- Buhari ba shi da tausayi, ya yi murabus kawai —Tsohon hadimin Ganduje
Kazalika, ya yi Allah wadai da dasa bam din da aka yi, inda ya ce lamarin ya jefa shi cikin dimuwa da bakin ciki mai tarin yawa.
“Kamar yadda ’yan Najeriya suke ji, na ji zafin faruwar wannan lamarin, wanda shi ne na biyu da ya yi sanadin mutuwar fasinjojin da ba a san adadinsu ba.
“Harin da aka kai kan jirgin kasa, abin takaici ne; kuma muna tare da iyalan wadanda suka rasu, sannan mun sanya wanda suka ji rauni a addu’a,” in ji Buhari.
Buhari ya kuma ba da umarnin a gaggauta sanya jami’an tsaro a dukkan hanyoyin jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna da kuma na Legas zuwa Ibadan.
Ya kuma umarci hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da su gaggauta gyara hanyoyin da suka lalace tare da ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum ba tare da bata lokaci ba.
Buhari ya bayar da wadannan umarni ne, bayan ya karbi bayanan da Manyan Hafsoshin Tsaro karkashin jagorancin Janar Lucky Irabor, da na kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, na sama, Air. Marshal Isiaka Amao, Sufeto-Janar na ’yan sanda, Usman Baba Alkali, da Manjo Janar Samuel Adebayo, da Shugaban Hukumar Leken Asiri da kuma Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi a Fadar Shugaban Kasa.
Har wa yau, ya kuma bukaci shugabannin hukumomin tsaron da su kubutar da dukkan fasinjojin da aka sace tare da tabbatar da cafko ’yan bindigar da suka kai harin.
Buhari, ya yabawa jami’an tsaro da jami’an agajin gaggawa kan gaggawar kai dauki ga wadanda suka samu rauni yayin harin.