Mace ta farko mai sharhin wasanni a Jihar Kano, Salamatu Yusuf, ta ce har kasar Amurka sai da ta gayyace ta saboda saboda kwarewarta a sharhin wasanni a kafar yada labarai.
Fitacciyar ’yar jaridar, wadda aka fi sani da Salma Sports, ta bayyana yadda gwamnan wata jiha ya yi mata tayin aiki da abubuwan alfarma don ta sauya sheka daga tawagar ’yan wasan Jihar Kano, amma ta ce a kai kasuwa.
- DAGA LARABA: Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Hukumar INEC
- Likitocin Najeriya Sun Koka Kan Yadda Ake Bautar Da Su A Birtaniya
Hajiya Salamatu ta bayyana yadda ta nuna wa abokan aikinta maza cewa ita ba kanwar lasa ba ce a harkar wasanni, “Daga baya har…suka daina ganin fagen (sharhin wasanni) nasu ne, saboda da sun fara zan nuna musu ni ma fa fagena ne.
“A haka aka zauna har da yawansu suka bar aiki da mu, suka koma wasu wauraren.”
A wata hira ta musamman da Aminiya, albarkacin zagayowar Ranar ’Ya Mace ta Duniya ta 2022, Salma Sportsa ta ce, kwarewarta kan sharhin wasanni ta sa, “Karshe ma dai har Amurka an kira ni dalilinsa, domin kin san shi wasa yare daya gare shi a duniya, na hadin kai.”
Fara wasanni da nasarori da ta samu
Salma Sports ta ce kafin ta fara sharhin wasanni a gidan rediyo sai da ta yi wasanni iri-iri tun daga kuruciya har zuwa girmanta.
“Ba na mantawa a shekarar a 1966 akwai gasar da na yi a Bauchi, har sai da na kai zagaye na karshe, kuma shi ne gasata ta farko a bangaren.
“Gwamnan har tayin aiki da abubuwan more rayuwa ya yi min don na koma can, amma na ki.”
Ta ce, “Na fara wasanni tun ina makaranatar firamare, lokacin ana gasar wasanni tsakanin makarantun firamare.
“Daga nan na fara wasanni a matakin jiha, har zuwa kasa.
“A shekarun 1970 ne karon farko na shiga gasar ninkaya, inda na wakilci Jihar Kano.
“Na shida na zo, kuma a lokacin ’yan Arewa sun dade ba su kai ko kusa da matakin ba.
“Na yi gasa sosai tsakanin ninkaya da judo; Haka kuma a shekarar 1977 na samu nasara lashe gwal da kofi daya.
“To amma fa a shekarar 1976, na samu lambar girmamawar gwal uku, azurfa daya, da tagulla daya.
“To fa kukan damuwar da na yi saboda samun tagulla da azurfan nan ne ya sa na dage a shekarar 1977 har na samu wannan kofin.
“Amma bayan an dawo daga gasar cin kofin kasa ta mata, na zo ta biyu.”
Bayan wasanni kafin fara sharhin wasanni
Salma Yusuf ta ce aikin da ta fara bayan ajiye wasanni shi ne na Hukumar Raya Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano, a matsayin Shugabar Sashen Raye-raye.
“Shi ma dai aikin hukumar na ajiye shi na koma kiwon kifi. Kuma ba wai karami na fara ba, don kwamin da na zuba kifin a Tiga, fadinsa ya kai a zura tirela biyu.
“Amma samun aikina na jarida ya sa na ajiye, don babu lokacin rike kasuwancin.
“Masu kula da gurin ma yawanci suna (harkar) wasanni. Sai na ajiye na dawo aikin rubuta labaran wasanni a gidan rediyo.
Kalubalen Bahaushiya mai harkar wasanni
Ta ce ba ta fuskanci kalubale ba sosai, kasancewar mahaifinta ya ba ta goyon baya har zuwa rasuwarsa.
Sai dai sauran iyaye da ’yan uwa sun sha yi mata fadan ta daina, amma ba ta daina din ba har sai da ta yi ra’ayi.
“Idan aka zo ana min fada sai na ce na daina a yi hakuri, amma fa washegari za a sake ji na na bulla a wani wasa.
“A haka dai har aka hakura aka kyale ni”, in ji ta.
Mace ta farko mai sharhin wasanni a Kano
Hajiya Salma Yusuf ta ce lokacin da aka gabatar da ita ga Shugaban Sashen Wasanni na gidan Rediyon Freedom a matsayin wacce za ta fara sharhin wasanni, duk sai da suka yi mamaki.
Ta ce, “Lokacin ba na mantawa Shugaban Sashin Ahmad Rufai Bello, har hira ya dauke ni da ita kan wasanni don ya ga da gaske na san harkar ko kuwa.
“Daga hirarmu ya fahimci da gaske na iya har muka fara.
“Kuma shi ne ya lakaba min Salma Sports, da ma Salma Yusuf din, domin da an sanni ne a matsayin Salamatu Yusuf.”
Ta ci gaba da cewa wani abokin aikinta ma yakan kira ta da Kallabi Tsakanin Rawuna, saboda ita kadai ke gogayya da maza a harkar wasannin.
“Daga baya har na saje suka daina ganin fagen nasu ne, saboda da sun fara zan nuna musu ni ma fa fagena ne.
“A haka aka zauna har da yawansu suka bar aiki da mu, suka koma wasu wauraren”, in ji Salma.
Jan hankalin iyaye kan harkar wasanni
“Ina jan hankalin iyaye kan hana ’ya’yansu mata shiga harkar wasanni, ya kamata su fahimci ba wai iya kwallon kafa ne kadai wasa ba, akwai su ninkaya da kwallon kwando da sauran wasannin da ba sai an bayyana jiki ba ko sabawa addini.
“Yanzu harkar ta tashi daga matsayin abin sha’awa ta zamo sana’a.
“Mutane na samun miliyoyin kudade dalilin wasanni a duniya – Kalli dai Serena Williams.
“Daga banagren sharhin wasanni ma ana samun alfanu sosai, domin ga shi dalilinsa na samu aikin da har tawa sana’ar na ajiye saboda shi.
“Har Amurka an kira ni dalilinsa, domin kin san shi wasa yare daya gare shi a duniya, na hadin kai.”