✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gode Allah da na fadi zaben Gwamna na 2015 – Akala

Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala ya ce ya gode wa Allah da Ya sa bai bar shi ya samu nasara a zaben…

Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala ya ce ya gode wa Allah da Ya sa bai bar shi ya samu nasara a zaben Gwamnan Jihar Oyo da aka gudanar a bara ba, inda ya ce ba zai iya hakuri da faduwar judin shiga da jihohi suke fuskanta a halin yanzu ba.
Otunba Alao-Akala ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci hedkwatar Jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja, inda ya ce ya je hedkwatar jam’iyyar ce domin tattaunawa da shugabannin jam’iyyar.
Tsohon Gwamna wanda ya fafata takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar Labour Party (LP) kuma ya sha kaye a hannun Gwamna Abiola Ajimobi, ya ce a matsayinsa na mai fama da cutar hawan jinni, bai san abin da zai yi bad a ya samu nasara a zaben.
Ya ce: “Na fadi haka ne, saboda ina tausaya wa gwamnoni, saboda halin da suka shiga a yanzu. Ba zan iya barci ba lura da faduwar kudin shiga na wata-wata. Wannan ne dalilin da ya san a fadi haka. Ban san yaya zan tunkari wannan matsala ba. Ina da cutar hawan jinni ban san me zan iya yi ba. Ina fata ba zan shiga matsalar da ta fi wannan ba.”
Game da ko zai tsaya takarar Gwamna a zaben shekarar 2019, Cif Alao-Akala ya ce: “Idan muka isa gada, sai a yi batun tsallake ta. Yanzu fa muna shekarar 2016 ce. Lokaci ne zai gaya wa kowa abin da yake son ya aikata. Me ya sa kuke son jarraba Ubangiji a kan shekarar 2019 tun yanzu? Kun san ko idan kuka yi barci yau za ku wayi gari gobe? Don haka a bar gobe ga Allah.”
Cif Akala ya bayyana gamsuwa kan canjin da gwamnati mai ci ke gudanarwa, nda ya ce, “Da ban gamsu ba, ba zan shiga Jam’iyyar APC ba. Ina da dammar yin zabi. Amma ina cikin APC ne saboda na gamsu da canjin da ta kawo. Shirin canji ya fara tuntuni. Yanzu ana gudanar da al’amura ba irin na baya ba ne. Abubwa sun fara canjawa. Kuma na san hakan na faruwa ne saboda cimma manufa mai kyau cikin rahamar Ubangiji. Kuma duk lokacin da ka zo gadon mulki ko wani mukami za ka iya haduwa da kalubale a nan da can. Amman an gaba kadan za mu maganace su.”